Bakonmu a Yau
Alhaji Mohammed Uba Garba na hukumar hana fasakwauri ta kan iyaka da ke Seme kan kame haramtacciyar shinkafar da ake shirin shigar da ita Najeriya
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:49
A Najeriya Hukumar hana fasakwauri da ke babbar kan iyakar kasar da Jamhuriyar Benin da ake kira mashigin Seme ta sanar da kame tarin haramtacciyar shinkafa da ake kokarin shigarwa Najeriyar daga ketare da kudinta ya tasamma biliyoyin naira.Alhaji Mohammed Uba Garba shine shugaban shiyyar Hukumar da ke Seme kuma ga abinda ya shaidawa Garba Aliyu Zaria.