Isa ga babban shafi
G5 Sahel

"Rundunar G5 Sahel ta zarce ta MINUSMA a Afrika"

Shugaban Mauritania Mohammed Ould Abdel Aziz ya ce, rundunar sojin Afrika ta Yamma da ke yaki da ‘yan ta’adda a Mali da ake kira G5 Sahel, ta zarce ta Majalisar Dinkin Duniya wato MINUSMA wajen aikin kakkabe ‘yan ta’adda.

Shugabannin kasashen G5 Sahel.
Shugabannin kasashen G5 Sahel. AFP PHOTO / IBRAHIM ADJI
Talla

Abdelaziz da ke shirin karbar bakwancin wani taron kaddamar da gidauniyar tallafa wa rundunar a ranar 6 ga watan gobe, ya ce duk da karancin kudi da kayan aikin da G5 Sahel ke da su, ayyukanta sun zarce na MINUSMA mai tarin kudade.

Shugaban ya ce, bai ga dalilin da ya sa kasashen duniya ke bai wa MINUSMA biliyoyin Dala ba duk da cewa ba a ganin tasirinta a kasa, yayin da ta G5 Sahel da ke kokari ba ta samun irin wadannan makuden kudade.

Rundunar G5 Sahel ta kunshi kasashen Mauritania da Burkina Faso da Chadi da Mali da Nijar da ke fama da tashe-tashen hankulan ‘yan ta’adda da suka hada da na Kungiyar Boko Haram.

Kasashen sun fada cikin tsananin rikici ne bayan tashin hankalin da ya barke a Libya a shekarar 2011 da kuma yadda ‘yan tawaye suka karbe iko da arewacin Mali a 2012, har ma da rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya.

Har ila yau, rundunar na taka rawa wajen tunkarar matsalar safarar mutane da kuma shige da fice tsakanin kasashe ba bisa ka’ida ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.