Isa ga babban shafi
Kamaru

An ceto daliban da aka yi garkuwa da su a Kamaru

Jami'an tsaron Kamaru sun yi nasarar ceto wasu dalibai tare da malaminsu da 'Yan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin da ke fama da tashin hankali.

Wasu Jami'an tsaron Kamaru
Wasu Jami'an tsaron Kamaru AFP/Alexis Huguet
Talla

Rahotanni sun ce, an sace daliban ne guda 9 da malaminsu guda a garin Kumba a ranar Talata kafin jami’an sojin suyi nasarar kubutar da su a ranar Laraba.

Bayanan da ke fitowa daga kasar sun ce, sojoji sun hallaka 'yan bindiga 4 tare da cafke guda a samamen da suka kai na ceto daliban makarantar.

Kungiyoyin ‘yan arawe masu dauke da makamai a yankin da ke magana da Turancin Ingilishi, sun bukaci al’ummarsu da su kaurace wa makarantun Boko har sai an gudanar da zaben raba gardama game da ballewarsu daga Kamaru.

Tun a bara ne, yankunan arewa maso yammaci da kuma kudu maso yammacin Kamaru suka fada cikin tashin hankalin ‘yan awaren, yayin da jami'an tsaron kasar ke ci gaba da murkushe su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.