Isa ga babban shafi
Najeriya

An Sako Yan tagwayen Zamfara

Rahotanni daga Najeriya sun ce mutanen da suka yi garkuwa da yan tagwayen jihar Zamfara guda biyu sun sake su, kuma yanzu haka sun koma gida.Jaridar Daily Nigerian tace tayi magana da yaran biyu wadanda suka tabbatar da cewar an sake su ba tare da sun samu rauni ba.

Yan Tagwayen Zamfara
Yan Tagwayen Zamfara AKA-CORR
Talla

Jaridar tace rahotan da ta samu ya tabbatar da biyan diyyar naira milyan 15 da jama’a suka bada taimako kafin sakin yaran.

Cikin wadanda suka bada taimako harda dan majalisar dattawa Sanata Kabir Marafa da ya bada naira miliyan 6, yayin da dangin yaran ta bakin wani dan uwan su Ibrahim Abubakar, yace sun sayar da kadarorin su da ya kai miliyan 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.