Isa ga babban shafi
Janhuriyar Tsakiyar Afrika

Mutane 37 Aka Kashe A Sabon Rikicin Janhuriyar Tsakiyar Afrika

Rahotanni daga kasar Janhuriyar Tsakiyar Afrika na cewa rayukan mutane akalla 37 suka salwanta sakamakon wani kazamin tarzoma daya sake barkewa a garin Aliandao inda aka dambace tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai.

Shugaban Janhuriyar Tsakiyar Afrika  Faustin-Archange Touadéra
Shugaban Janhuriyar Tsakiyar Afrika Faustin-Archange Touadéra rfi
Talla

Kafofin samun labarai na Majalisar Dinkun Duniya na gaskata rasa rayukan.

Wasu bayanan na cewa mayaka kiristoci anti- Balaka suka fara kashe mutane bakwai, kafin kungiyar anti-Seleka ta mayaka musulmi suka maida martini.

Tun Alhamis aka fara tarzoma sakamakon kashe wani limamin Kirista  a garin Aliandao wanda Kiristoci ke zargin Musulmi da aikatawa.

Wannan kasa dake fama da matsanancin talauci duk da albarkatun arzikin karkashin kasa da Allah ya bata, ta fara fuskantar tarzoma ba kangado ne tun shekara ta 2013 bayan kifar da Gwamnatin Shugaba Francois Bozize wanda kirista ne, wanda ake zargin kungiyar musulmi da ake kira anti-seleka da mamaye Gwamnatin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.