Bakonmu a Yau
Tsohon sarkin gwandu Mustapha Haruna Jokolo kan garkuwa da 'Yan mata biyu a Zamfara
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:32
Duk da matakin girke tarin Soji da Hukumomin Najeriya suka yi a jihar Zamfara da nufin samar da tsaro, al’amura masu alaka da garkuwa dama kisan jama’a na ci gaba da tsananta.Kusan garkuwar baya-bayan nan da ta tayar da hankalin al’ummar jihar bai wuce sace yaran nan mata ‘yan biyu da ‘yan bindigar suka yi ba, tare da neman a biyasu diyyar miliyan 150 kafin sakinsu duk kuwa da kasancewarsu marayu kuma masu karamin karfi.Tsohon sarkin gwandu Mustapha Haruna Jokolo na daga cikin wadanda ke yawan magana kan wannan batu ya kuma yi tsokaci kan hakan.