Isa ga babban shafi
Kamaru

An kashe mayakan aware 25 a Kamaru

Wata majiyar tsaro a kasar Kamaru ta tabbatar cewa, akalla mayakan 'yan aware 25 ne aka kashe a wani fada da suka gwabza da dakarun gwamnati a yankin nan da ke amfani da Turancin Inglishi da ke arewa maso gabashin kasar.

Wasu daga cikin sojojin Kamaru a yankin masu magana da Turancin Ingilishi
Wasu daga cikin sojojin Kamaru a yankin masu magana da Turancin Ingilishi REUTERS/Joe Penney
Talla

Mayakan 25 da ake kira Amba boys sunan da ake kiran 'yan awaren kasar da shi, an kashe su ne a cikin wasu jerin fadace-fadace guda uku da suka gwabza a ranar Laraba a kauyen Mbot da ke kusa da garin Nkambe, kamar yadda majiyar tsaron a Yaounde babban birnin kasar ta sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP.

A hoton da AFP ya samu daga wata majiyar tsaro a yankin arewa maso yammaci kasar ta Kamaru, an nuna gawarwakin mutane da dama da kuma aka gabatar a matsayin na 'yan awaren da aka kashe. Sannan kuma  an ajiye  makamansu a kusa da gawarwakin.

Majiyar ta kara da cewa 'yan awaren sun kafa sansaninsu ne a cikin wata makarantar gwamnati da ke Mayo Binka, 'yan kilomitoci daga Nkambe.

Mark Bareta, daya daga cikin manyan masu farfagandar 'yan awaren, ya sanar a shafinsa na Facebook da ya samu tsokacin kimanin mutane dubu 100 cewa, yaki da ake gwabzawa a yankin na Inglishi gaskiya ne, sun kuma tafka asara. Kuma fadan ya yi zafi a Donga Mantung, da ke cikin jihar ta Nkambe babban birnin yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.