Harin ta'addanci ya hallaka mutane da dama a Somalia
Akalla mutane 20 suka mutu yayinda da dama suka jikkata bayan tashin wasu bama-bamai da aka sanya cikin motoci a birnin Mogadisho na kasar Somaliya, yau juma’a.
Wallafawa ranar:
Majiyoyin labarai a kasar ta Somaliya sun tabbatar da cewa galibin mutanen da suka mutu a harin na yau fararen hula ne sai kuma tsirarun jami’an tsaro da ke kan hanya.
A cewar Ibrahim Mohammed babban jami’in dan sanda mai kula da birnin na Mogadisho, bama-baman biyu an sanya su ne a cikin Mota kuma bayan tashinsu ne na ukun ya kara ta shi a wani waje daban.
Wani ganau Hasan Adan, ya ce akasarin wadanda abin ya rutsa da su, mutane ne da ke tafe a cikin kananan motoci.
Kawo yanzu dai babu kungiyar da ta dauki alhakin harin sai dai akwai kwakkwaran zaton cewa kungiyar Al-Shebab ce ta kaddamar da shi, la'akari da yadda ta sha alwashin ganin bayan gwamnatin kasar ta Somaliya, mai samun gowon bayan kasashen duniya da ma sojojin kungiyar hadin kan Afrika dubu 20.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu