Uganda za ta fara riga-kafin Ebola kan jami'anta na Lafiya
Hukumomin lafiya a Uganda sun sanar da aniyar fara gangamin rigakafin cutar Ebola a jibi Litinin don kaucewa barkewar cutar la’akari da yadda ake ci gaba da fuskantar annobarta a makociyar kasar Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo.
Wallafawa ranar:
A cewar ma’aikatar lafiyar Uganda yanzu haka za ta fara bayar da rigakafin ne daga kan jami’an lafiyarta musamman wadanda ke aiki gab da kan iyakar jamhuriyyar Demokradiyyar Congo tazarar mil 62 da yankin da ake fuskantar annobar.
Ministan lafiyar Uganda Jane Ruth Aceng ya ce yanzu haka sun aike da allurai dubu 2 da dari 1 ga jami’ansu da ke can kan iayakar kasar don bayar da kariya ga lafiyarsu kafin kai tsaye su dawo kan jami’ansu da ke aikin a cikin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu