Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta kai kazamin hari a kauyukan Borno

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun kashe mutane da dama tare da tilasta wa daruruwa tserewa daga gidajensu bayan wani hari da suka kaddamar a karamar hukumar Koduga da ke jihar Bornon Najeriya.

Shugaban mayakan Boko Haram Abubakar Shekau da mukarrabansa
Shugaban mayakan Boko Haram Abubakar Shekau da mukarrabansa AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Rahotanni na cewa, maharan sun kutsa cikin kauyukan Kofa da Bulabbrin da misalin karfe 7:50 na daren da ya gabata, in da suka yi ta kiran “ Allahu Akbar” a dai dai lokacin da suke barin wuta kan jama’a.

Kazalika mayakan sun kona kauyukan kamar yadda wadanda suka shaida aukuwar lamarin suka tabbatar.

Rundunar ‘Yan Kato da Gora ta ce, ta yi kokarin tunkarar mayakan amma suka fi karfin ta ganin yadda suka yi ta barin wuta ta sama.

A halin yanzu, daruruwan jama’ar da suka rasa muhallansu sakamakon tashin hankalin na baya-bayan nan na samun mafaka a Dalori.

Kawo yanzu, jami’an tsaron kasar ba su yi tsokaci game da farmakin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.