Isa ga babban shafi
Wasanni

FIFA ta haramtawa tsohon shugaban kwallon Ghana aiki har abada

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta zartas da hukuncin haramtawa tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Ghana Kwesi Nyantakyi, shiga dukkanin al’amuran da suka shafi wasanni har abada.

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Ghana Kwesi Nyantakyi.
Tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Ghana Kwesi Nyantakyi. REUTERS
Talla

Kari kan haramcin, Nyantakyi zai kuma biya tarar euro dubu 390.

Hukumar ta FIFA ta ce daukar matakin ya biyo samun Nyantakyi da laifin cin hanci da rashawa da kuma karya wasu ka’idojinta.

FIFA ta soma bincikar tsohon shugaban kwallon kafar na Ghana, bayan da Anas Armaya’u Anas, wani dan jarida da ya batar da kama, ya dauki hotonsa lokacin da yake karbar cin hancin dala dubu 65,000 daga gare shi.

Sai dai tsohon shugaban ya musanta karbar na goron, inda ya ce an hada hoton ne domin bata masa suna.

Wannan dambarwa ce ta tilastawa Kwesi Nyantakyi sauka daga mukamansa da suka hada da na shugabancin hukumar kwallon kafa ta Ghana, mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika CAF, da kuma barin matsayinsa na dan majalisar koli a hukumar FIFA.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.