Isa ga babban shafi
Algeria

Bouteflika zai sake yiwa Jam'iyyarsa takara a 2019

A yau lahadi Sakatary jam`iyya mai mulkin kasar Algeria Djamel Ould Abbes ya bayyana cewa jam`iyyar su ta tsayar da Shugaban kasar mai ci Abdel Aziz Bouteflika mai shekaru 81 a matsayin dan takarar ta a zaben watan Afrilun shekarar 2019.

Abdelaziz Bouteflika, Shugaban kasar Algeria
Abdelaziz Bouteflika, Shugaban kasar Algeria © Canal / AFP
Talla

A watan Maris na shekara ta 2014 ne akalla mutane 100 suka janye daga shiga takarar zaben shugabancin kasar Algeria yayin da ake ci gaba da sukar takarar Abdel’aziz Bouteflika wanda ya kwashe shekaru 15 yana shugabanci a kasar.

Bouteflika, ya bayyana kudirin tsayawa takara a shekara ta 2014 a kafar Talabijin wanda shi ne karon farko da shugaban ya fito a bainar Jama’a tun lokacin da ya dawo daga jinya a asibitin kasar Faransa.

Kasar Algeria dai ta yi kokarin kaucewa juyin juya halin da ya rutsa da sauran kasashen larabawa irinsu Libya da Tunisia da Masar wanda ya ke daya daga cikin nasarorin da ake dangatawa da shugaba Bouteflika da ke fama da rashin lafiya yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.