Yan Sanda sun tarwatsa taron masu zanga-zanga a Conakry
A kasar Guinea wani yaro ya rasa ransa a lokacin da ‘yan sanda suka tarwatsa masu zanga-zanga tareda yin amfani da barkonun tsohuwa a birnin Conackry.
Wallafawa ranar:
A kokarin tarwatsa su a Conakry,ana zargin jami`an tasro da kokarin kasha jagoran yan adawa wanda ya bayyana cewa sun harbi motarsa a lokacin gangamin don adawa da zaben kasar.
Mamacin dan shekaru 18 mai suna Mamadou Samba Diallo na koyon aikin kafinta ne
Dan uwan mamacin ya bayyana cewa akan idanunsa aka bindige dan uwan nasa har lahira kuma jamian tsaron bayan da suka tabbatar da ya mutu suka kama gabansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu