Bakonmu a Yau
Mazi Obinna Ofarima kan bayyanar Nnamdi Kanu bayan fiye da shekara guda
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:20
A cikin karshen makon da ya gabata shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra a Najeriya Nnamdi Kanu ya bayyana kansa a cikin wani bidiyo da ke nuna shi yana ibada a birnin Qudus fiye da shekara guda bayan daina jin duriyarsa.Cikin Faifan bidiyon na Nnamdi Kanu ya bukaci al'ummar Igbo su kauracewa zaben 2019 da ke karatowa a Najeriyar nan da 'yan watanni.Hakan yasa muka tattauna da Mazi Obinna Ofarima wani jagora a kabilar ta Igbo ga kuma abin da ya ke cewa.