Isa ga babban shafi
Kamaru-Zabe

An shiga rana ta uku da fara sauraron shari'ar magudin zabe a Kamaru

An shiga rana ta uku da kotun tsarin mulki ke sauraren korafe-korafe dangane da zaben shugabancin kasar da aka gudanar ranar 7 ga wannan wata a Kamaru, inda wasu ‘yan takara daga bangaren adawa ke zargin tafka magudi.

Bangarorin adawa a kasar ta Kamaru na zargin gwamnati mai ci da tafka magudi a zaben na ranar 7 ga wata.
Bangarorin adawa a kasar ta Kamaru na zargin gwamnati mai ci da tafka magudi a zaben na ranar 7 ga wata. AFP/Pool/Lintao Zhang
Talla

An dai cigaba da tafka mahawara cikin zauren kotun, inda lauyoyi 16 da ke kara Maurice Kamto daya daga cikin masu adawa da shugaba Paul Biya ke zargin cewa sakamakon zaben da aka tattaro daga mazabu 32 na cike da magudi.

A wadannan mazabu kawai akwai masu kada kuri’a sama da milyan daya da dubu 300 daga cikin milyan 6 da dubu 600 da ake da su a fadin kasar.

Lauyan Kamto mai suna Emmanuel Simh, ya bukaci hukumar zaben kasar Elecam ta ba su damar isa ga sakamakon wadannan mazabu, bukatar da shugaban kotun mai shari’a Clément Atangana ya yi watsi da ita.

Mataimakin Shugaban hukumar zaben kasar Abdoul Karimou, ya ce duk wani dan takara da ya san abin da ya ke yi, ya kamata a ce yana da masaniya dangane da illahirin rahotanni guda dubu 25 da wakilai hukumar zabe da ma na sauran jam’iyyun siyasar kasar suka sanya wa hannu a ranar zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.