SERAP, PDP sun soki shugaba Buhari kan hana mutane 50 fita daga Najeriya
Kungiyar SERAP da ke fafutukar tabbatar da adalci a Najeriya, ta bayyana matakin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya dauka na hana wasu mutane 50 da ake zargi da rashawa ficewa daga kasar da cewa ya saba wa doka.
Wallafawa ranar:
Kungiyar ta SERAP ta bukaci shugaban kasar da ya cire wannan haramci, domin an dauke shi ne ba tare da mutunta dokokin Najeriya ba kamar yadda kungiyar ta SERAP ta ce.
Ita ma babbar jam’iyyar adawa ta kasar PDP ta bayyana kudurin da shugaban kasar ya yi amfani da shi a matsayin wanda ya yi hannun riga da dokokin kasar, tana mai cewa shugaban ya dauki matakin ne domin muzgunawa ‘yan adawa.
A ranar asabar da ta gabata ne shugaba Muhammadu Buhari ya yi amfani da kuduri mai lamba 6, domin hana mutanen 50 ficewa daga kasar, saboda zargin rashawa da ake yi masu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu