Isa ga babban shafi
Kamaru-'Yan ware

Lauyoyin yan aware a Kamaru sun bukaci a saki shugabansu, Julius Ayuk Tabe

Wani gungun lauyoyin kasar Kamaru ya bukaci sakin shugaban yankin yan awaren dake amfani da Inglishi Sisiku Julius Ayuk Tabe da wasu makarabai 9 da aka kama su tare a Najeriya. kafin a tiso keyarsu a kamaru a watan janairun da ya gabata.

Shugaban kasar Kamaru  Paul Biya.
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya. AFP
Talla

Shugaban gungun lauyoyin masu kare shuwagabanin yankin yan aware dake amfani da turancin Inglishi, John Fru Nsoh ya sanar da kamfanin dillancin labaran Afp cewa, an kama Ayuk Tabe ne ba a kan ka’ida ba a Najeriya, kuma aka dauko shi a cikin mummunan yanayi, ta hanyar sanyo shi a jirgin sama ba tare da damarar da ta daure shi a kujerar jirgin ba.

Su dai gungun lauyoyin, sun shigar da korafin nasu ne a gaban kotun daukaka kara da ke Yaounde babban birnin kasar ta Kamaru, inda suke fatan a salami Ayuk Tabe da sauran shuwagabanin yankin yan awaren ta hanyar bayyana su a matsayin marasa laifi.

A baya dai karamar kotu ta yi watsi da bukata da lauyoyin suka gabatar mata, da kuma ya kamata kotun koli ta yi nazarta a jiya Alhamis, kafin ita ma daga bisani ta sake daga sauraren shara’ar har zuwa ranar daya ga watan nowamban mai zuwa, sakamakon abinda ta kira kan rashin halartar wadanda ake zargin a gabanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.