Isa ga babban shafi
Kamaru

Ana dakon tattara sakamakon zabe a Kamaru

Al’ummar Kamaru sun soma dakon sakamakon zaben shugabancin kasar, bayan kammala kada kuri'unsu a ranar Lahadi, 7 ga watan Oktoba, 2018.

Wata mata yayin kada kuri'arta a wata rumfar zabe dake birnin Yaounde. (7/10/2018)
Wata mata yayin kada kuri'arta a wata rumfar zabe dake birnin Yaounde. (7/10/2018) REUTERS/Zohra Bensem
Talla

A halin yanzu dai za’a cigaba da dakon kammala kidaya da kuma bayyana sakamakon zaben, wanda dokar kasar ta fayyace cewa tilas a bayyana shi a cikin kwanaki 15 nan gaba.

Yayin gudanar da zaben na yau, wata majiyar tsaron kasar ta kamaru ta rawaito cewa, a Bamenda, dake yankin arewa maso yammacin kasar mai fama da rikicin ‘yan aware, saida jami’an tsaro sun harbe wasu ‘yan ‘yan bindiga, 3, baynda suka bude wuta kan jama’a suka kuma tsere a bisa babur, daga bisani kuma sojin Kamaru suka cimmusu.

To sai dai rahotanni daga yankin arewa mai nisa mai fama da rikicin Boko Haram, sun ce zaben shugabancin kasar na yau, ya gudana cikin tsauraran matakan tsaro, ba tare fuskantar cikas ba.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne aka samu kawance jam’iyyun FDP da MRC, irinsa na farko da aka taba gani a kasar tun bayan na shekarar 1992.

Jam’iyyun na FDP da MRC sun cimma yarjejeniyar ce, bayan da dan takarar FDP Akere Muna, ya amince da janye takararsa don marawa Maurice Kamto na MRC baya, domin kayarda shugaba mai ci Paul Biya, mai shekaru 85 dake neman zarcewa wa'adi na shida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.