Isa ga babban shafi
Kamaru-'Yan ware

Halin da ake ciki kan shirin zaben shugabancin Kamaru

Sama da mutane milyan 6 da rabi ne suka cancanci kada kuri’unsu a zaben da za a yi ranar Lahadi mai zuwa a Kamaru. Sai dai zaben zai gudana ne a cikin wani yanayi na rashin tsaro musamman a yankunan ‘yan aware da ke amfani da Turancin Ingilishi.

Buea, babban birnin yankin kudu maso yammacin Kamaru, zalika cibiyar rikicin 'yan aware masu amfani da turancin Ingilishi, dake neman ballewa daga kasar. 27 ga watan Afrilu, 2018.
Buea, babban birnin yankin kudu maso yammacin Kamaru, zalika cibiyar rikicin 'yan aware masu amfani da turancin Ingilishi, dake neman ballewa daga kasar. 27 ga watan Afrilu, 2018. © ALEXIS HUGUET / AFP/Archives
Talla

Hukumar zaben kasar Elecam, ta ce za a gudanar da zaben a cikin rumfuna sama da dubu 25 a sassa daban daban na kasar, kuma sama da rumfuna dubu 4, suna yankuna biyu na ‘yan aware ne da ke fama da ‘yan bindiga, wadanda suka yi barazanar hana gudanar da zaben.

Adadin masu kada kuri’a a yankunan ‘yan awaren kamar yadda alkalumman hukumar zabe suka nuna ya kusa milyan daya da rabi, sai dai akwai shakku dangane da yadda mahukunta za su isar da kayayyaki da kuma jami’an zabe a wadannan yankuna, yayin da jama’a ke dari-dari wajen fita domin kada kuri’unsu saboda dalilai na rashin tsaro.

‘Yan aware da suka tsananta kai hare-hare cikin a ‘yan watannin baya-bayan nan, sun yi barazanar afka wa duk wanda ya yi gangancin fita don yin zaben a ranar ta Lahadi, yayin da aka kiyasta cewa akwai wasu dubban mutane da tuni suka bar gidajensu sakamakon wannan rikici.

Matsalar tsaro ba wai ta takaita ne a yankunan ‘yan awaren kasar kawai ba, domin kuwa akwai wasu dubun dubatar mutanen da suka bar gidajensu musamman a yankin Arewa mai nisa sakamakon rikicin Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.