Isa ga babban shafi
Mali

Rundunar G5 Sahel ta sauya mazaunin hedikwatarta zuwa Bamako

Rundunar hadin gwiwar kasashe biyar mai yakar ta’addanci ta G5 Sahel da ke Mali, ta mayarda hedikwatarta babban birnin kasar Bamako, daga garin Sevare.

Tsohuwar shalkwatar rundunar G5 a Sevare na kasar Mali
Tsohuwar shalkwatar rundunar G5 a Sevare na kasar Mali REUTERS/Adama Diarra
Talla

A Juma'ar nan ce Hfsan soji na kasar Mauritania mai shugabantar rundunar ta G5 Sahel Janar Hanena Ould Sidi ya sanar da canza hedikwatar rundunar daga garin Sevare zuwa Bamako.

Matakin sauya mazaunin hedikwatar ya biyo bayan, harin kunar bakin waken da ya hallaka sojoji biyu da farara hula guda, da aka kai Hedikwatar a ranar 29 ga watan Yuni, wanda masu tada kayar baya da sukai wa Al’qaeda mubaya’a suka yi ikirarin kaiwa.

Wata majiya daga rundunar hadin gwiwar ta kasashen Mali, Chadi, Niger, Burkina Faso da Mauritania, ta ce sauyin ya zama tilas saboda komawa wajen da yake da saukin sadarwa, zalika sojin Faransa ma sun tabbatar da wannan sauyi.

A ranar 23 ga watan Fabarairu na shekarar da muke ciki, manyan kasashen duniya sukai alkawarin taimakawa rundunar da kimanin euro miliyan 420, sai dai har yanzu ana fuskantar tsaiko wajen cika alkawarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.