Isa ga babban shafi
Najeriya-Duniya

Buhari ya sake janyo hankalin Duniya kan tafkin Chadi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake shaidawa shugabannin kasashen duniya irin matsalar da sauyin yanayi ta haifar wajen tsukewar tafkin Chadi wadda mutane sama da miliyan 45 suka dogara da shi domin rayuwa.

Shugaban Najeriya Mahamadu Buhari, a zauren Majalisar Dinkin Duniya
Shugaban Najeriya Mahamadu Buhari, a zauren Majalisar Dinkin Duniya RFI hausa
Talla

Yayin jawabi a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 73, shugaba Buhari yace tsukewar tafkin ya haifar da matsaloli da dama da suka hada da jefa mutanen yankin cikin rashin ayyukan yi da rikici tsakanin manoma da makiyaya da kuma matsalar yan ta’adda.

Shugaban ya tabo batutuwa da dama a jawabin sa da suka hada da rikicin Syria da Yemen da rikicin kabilanci da addini a sassan duniya, da rikicin Isra’ila da Falasdinu da halin da yan kabilar Rohingya dake Myanmar suke ciki, yaki da boko haram da kuma cin hanci da rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.