Isa ga babban shafi
Kamaru

Fursunoni 80 sun tsere daga gidan yarin Kamaru

Akalla Fursunoni 80 sun tsere daga wani gidan yarin da ke yankin masu magana da turancin Ingilishi a Kamaru bayan wasu ‘yan bindiga sun kai wa gidan hari a cikin daren da ya gabata.

Mutane 80 sun tsere daga gidan yarin Kamaru
Mutane 80 sun tsere daga gidan yarin Kamaru The News Nigeria
Talla

Wasu majiyoyi sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa, kimanin mutane 100 ke kulle a gidan kason da ke garin Wum mai tazarar kilomita 70 daga arewacin Bamenda, amma 80 suka arce.

‘Yan bindigan sun yi amfani da tsani wajen tsallaka garun gidan yarin kafin daga bisani su yi fata-fata da kofarsa.

‘Yan awaren Kamaru na gwagwarmayar kafa kasar Ambazonia mai cikakken ‘yanci, yayin da suka lashi takobin hana gudanar da zaben shugaban kasa a yankinsu.

A ranar 7 ga watan Oktoba ne za a guadnar da zaben shugaban kasa a Kamaru, in da ‘yan takara takwas ke fafatawa da shugaban kasa mai ci Paul Biya wanda ya mulki kasar tsawon shekaru 35, yayin da yake neman tazarce a karo na bakwai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.