Isa ga babban shafi
Wasanni

Pinnick ya lashe zaben shugabancin hukumar kwallon Najeriya

An sake zaben Amaju Pinnick domin ci gaba da jagorancin Hukumar Kwallon Kafar Najeriya NFF, a taron da masu ruwa da tsakani a harkar kwallon kafar kasar suka gudanar a wannan Alhamis a birnin Katsina.

Amaju Pinnick shugaban hukumar kwallon kafar Najeriya
Amaju Pinnick shugaban hukumar kwallon kafar Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo Supplied by Action Images
Talla

Pinnick ya yi nasarar lashe zaben ne da kuri’u 34, in da Aminu Maigari ya samu kuri’u 8, tsohon dan wasan Super Eagles, Tayo Ogunjobi ya samu kur’i biyu sai kuma Chinedu Okoye da bai samu ko da kuri’a daya ba.

Kafin wannan zabe dai Hukumar Kwallon Kafar Najeriya ta tsunduma a cikin rikicin shugabanci tsakanin Pinnick da kuma Chris Giwa, lamarin da ya sa Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA tsoma baki domin kawo karshen rikicin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.