Isa ga babban shafi
Burkina-Faso

Mayakan jihadi sun hallaka mutane 8 a Burkin Faso

A kalla fararen hula 8 ne suka rasa rayukansu a tsakanin daren juma’a 14 kawo safiyar assabar 15 ga watan satumba 2018, a wani harin ta’addanci da aka kai a gabashin kasar Burkina Faso, yankin da mayakan dake ikararin jihadi suka kwashe tsawon watanni sun shuka ta’asa, kamar yadda mahukumtan wannan yanki suka sanar.

sojojin Burkina Faso a gaban gidan da aka yi zargin yan ta'adda na ciki a 22 mayu 2018.
sojojin Burkina Faso a gaban gidan da aka yi zargin yan ta'adda na ciki a 22 mayu 2018. RFI / Yaya Boudani
Talla

Kasar da ta kasance mai makwabtaka da kasashen Mali da jamhuriyar Nijar, Burkina Faso ta dau tsawon lokaci ba tare da kungiyoyin dake dauke da makamai a yankin sahel sun farmata ba, amma shekaru uku da suka gabata kasar na fuskantar hare hare daga kungiyoyin dake ikrarin jihadi, ala’amarin dake haddasa hasarar rayukan mutane.

Ofishin gwamnan yankin da lamarin ya faru ya ce, a cikin daren juma’a 14 zuwa safiyar assabar 15 ga watan satumba shekara 2018 ne, aka kai hare haren biyu a garuruwan Diabiga Km 60 da kuma Kompienbiga mai tazarar km 15 da Pama babban birnin yankin gabashin kasar ta Burkina Faso inda mutane 8 suka kwanta dama wasu 5 kuma suka jikkata

A cewar majiyar tsaro da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya zata da ita a Wagadugu babban birnin kasar, harin farko an kai shi ne kan wani shugaban addini da magoya bayansa, inda mutane 5 da suka hada da shugaban na Addini suka rasa rayukansu tare da jikkata wasu 3. A yayin da hari na 2, aka kai shi garin Kompienbiga, inda mutane 3 iyalin gida guda suka kwanta dama, wasu 2 kuma suka jikkata

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.