Isa ga babban shafi
Tanzania-Haihuwa

Magafuli ya bukaci mata su daina shan maganin hana haihuwa

Shugaban Tanzania John Magufuli, ya bukaci matan kasar su dai na amfani da maganin hana haihuwa saboda a cewarsa ana bukatar samun cigaba da haihuwa a kasar

Magufuli ya bukaci Al'ummar kasar ta Tanzania da su yi watsi da shawarwari marasa amfani da mutanen wasu kasashen ke basu kan tazarar iyali.
Magufuli ya bukaci Al'ummar kasar ta Tanzania da su yi watsi da shawarwari marasa amfani da mutanen wasu kasashen ke basu kan tazarar iyali. REUTERS/Sadi Said
Talla

A cewar Shugaba Magufuli bai ga dalilin yin amfani da magunguna hana haihuwa a kasar wadda ke da karfin noma ba, kuma galibin matan karkara sun yi shura wajen noma da kiwo, wanda cikin sauki za su iya ciyar da duk yawan 'ya'yan da su ke da shi ba tare da fuskantar matsala ba.

Shugaban ya ce ya zagaya a sassa daban daban na duniya ciki har da kasashen Turai, kuma ya gano irin illolin da shan kwayoyin hana haihuwa suke haddasawa ga kasashen da ke ikirarin ci gaba, inda a yau su ke fama da karancin jama’a da kuma rashin ma’aikata.

Magufuli ya bukaci Al'ummar kasar ta Tanzania da su yi watsi da shawarwari marasa amfani da mutanen wasu kasashen ke basu kan tazarar iyali, yana mai cewa abu ne mai muhimmanci a ci gaba da samun haihuwa a Kasar.

Tanzania dai na da yawan jama’a da adadin su ya kai miliyan 60, kari a kan miliyan 10 da suke da su lokacin samun yanci a shekarar 1961.

Majalisar Dinkin duniya na hasashen cewa, nan da shekarar 2050 yawan al'ummar Afrika zai ninka zuwa biliyan 2 da rabi, matakin da ke matsayin barazana ga tattalin arzikin kasashen musamman wadanda basa samun habakar da ta kamata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.