Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Mutane 19 sun mutu a hadarin jirgin saman Sudan ta kudu

Hukumomi a Sudan ta kudu sun tabbatar da mutuwar mutane 19 bayan faduwar wani jirgin sama daya dakko fasinja daga Juba zuwa birnin Yirol yau Lahadi.

Rahotanni sun ce uku daga cikin wadanda suka mutu a hadarin jirgin kananan yara ne.
Rahotanni sun ce uku daga cikin wadanda suka mutu a hadarin jirgin kananan yara ne. REUTERS/Stringer
Talla

Ministan yada labaran kasar Taban Abel ya shaidawa manema labarai cewa jirgin na dauke ne da Fasinja 23 kuma yazu haka an gano gawar mutane 19 sai kuma biyu da suka tsira da ransu, yayinda har yanzu ake nema mutane 2.

A cewar minstan guda cikin mutanen da suka tsira da rayukansu wani likita ne dan asalin kasar Italiya da ke aiki da kungiyoyin bayar da agaji a kasar kuma yanzu haka yana cikin mawuyacin hali yayinda ya ke karbar kulawa a babban asibitin birnin Yirol.

Rahotanni sun ce jirgin ya fadi ne a gab da gabar ruwan lamarin da ya sa galibin wadansa suka mutu an tsamo gawarsu ne a cikin ruwan, haka zalika 3 daga cikin wadanda suka mutun kananan yara ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.