Isa ga babban shafi
Madagascar

Shugaba Hery na Madagascar ya ajje mukaminsa don tsayawa takara

Shugaban Kasar Madagascar Hery Rajaonarimampianina ya sauka daga mukamin sa yau juma’a, domin shiga takarar zabe mai zuwa, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Kundin tsarin mulkin kasar ta Madagascar bai sahalewa shugaba takarar neman zabe yana kan karagar mulki ba.
Kundin tsarin mulkin kasar ta Madagascar bai sahalewa shugaba takarar neman zabe yana kan karagar mulki ba. Reuteurs/Lintao Zhang
Talla

Kundin ya bukaci shugaban kasa ya sauka daga mukamin sa watanni biyu kafin zaben da za’ayi ranar 7 ga watan Nuwamba, kuma zai fafata ne tare da yan takarar da dama, cikin su harda tsohon shugaban kasa Andry Rajoelina.

Yayin jawabi ga al’ummar kasar, shugaban yace musu lokaci yayi da zai sauka domin mutunta dokar kasa, kuma ya mika takardun sa ga kotun tsarin mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.