Isa ga babban shafi
Uganda-Amurka

Bobi Wine zai bar Uganda zuwa Amurka don duba lafiyarsa

Babban lauyan da ke kare fitaccen mawakin kasar Uganda da ya juye zuwa siyasa Bobi Wine ya ce mawakin zai tafi duba lafiyarsa kasar Amurka bayan zargin azabtarwa a hannun jami’an tsaron kasar sakamakon kamen da aka yi masa.

Akwai dai zargin cewa Jami'an sojin Uganda sun azabtar da Bobi Wine yayin kamen farko da suka yi masa matakin da ya sa dole ya fita Amurka don duba lafiyarsa.
Akwai dai zargin cewa Jami'an sojin Uganda sun azabtar da Bobi Wine yayin kamen farko da suka yi masa matakin da ya sa dole ya fita Amurka don duba lafiyarsa. STRINGER / AFP
Talla

Lauyan na sa Nicholas Opiyo ya ce hukumomin tsaron kasar sun kara cafke Bobi Wine mai shekaru 36 a jiya ne lokacin da ya ke kokarin barin kasar inda ya shafe daren jiyan a wani asibitin gwamnati, yayinda suke saran yau da misalin 11 dare ya bar Ugandan zuwa Amurka.

Sai dai hukumomi a Ugandan na zargin Wine da cin amanar kasa bayan jifan motar shugaba Yoweri Museveni yayin wani gangamin yakin neman zabe.

Kasashen Duniya dai sun gargadi Uganda kan matakin azabtar da Bobi ko dama da kansa babban Jojin kasar ya yi gargadi kan azabtarwa yana mai cewa hurumin Jami'an kawai kamawa ne amma ba azabtarwa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.