Isa ga babban shafi
Afrika-Rikici

Rikici ya hallaka fiye da yara miliyan 5 cikin shekaru 20 a Afrika

Wani binciken masana ya ce yake-yaken da aka gwabza a Afirka sun yi sanadiyyar mutuwar yara sama da miliyan 5 a cikin shekaru 20, saboda yadda tashin hankalin ya hana su zuwa asibiti domin samun kulawar da ta dace.

Rahoton ya nuna yadda tashe-tashen hankula a Najeriya da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ya lakume rayuka masu tarin yawa fiye da na sauran kasashen na Afrika.
Rahoton ya nuna yadda tashe-tashen hankula a Najeriya da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ya lakume rayuka masu tarin yawa fiye da na sauran kasashen na Afrika. Daily Trust
Talla

Rahotan binciken da aka wallafa a Jaridar Lafiya ta The Lancet ta yi nuni da yadda tashin hankalin da aka gani a kasashen Najeriya da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo tsakanin shekarar 1995 zuwa shekarar 2015 ya lakume tarin rayuka.

Eran Bedavid, daga Jami’ar Standford da ya jagoranci binciken ya ce alkaluman sun hada da yara miliyan 3 da ke kasa da shekara guda.

Binciken ya yi nazari ne kan tashe-tashen hankula 15,500 daga cikin kasashe 34 na nahiyar ta Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.