Isa ga babban shafi
Najeriya-Turai

Buhari ya nuna rashin goyon baya ga masu zuwa Turai ba bisa ka'ida ba

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi gargadin cewa basa goyon bayan duk wani yunkuri na tsallakawa Nahiyar Turai ba bisa ka’ida ba da wasu ‘yan kasar ke yi don samun rayuwa mai inganci.

Haka zalika Muhammadu Buhari ya sha alwashin dawo da ‘yan Najeriyar da suka makale a Libya a kokarinsu na tsallakawa nahiyar Turai ta tekun Maditerranean.
Haka zalika Muhammadu Buhari ya sha alwashin dawo da ‘yan Najeriyar da suka makale a Libya a kokarinsu na tsallakawa nahiyar Turai ta tekun Maditerranean. RFIHAUSA
Talla

Shugaban na Najeriya yayin ganawarsa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a fadarsa ta Villa da ke Abuja babban birnin kasar, ya ce duk hadarin da ‘yan ciranin za su fada ba ruwan gwamnatinsa da su.

A cewarsa kamata ya yi ‘yan Najeriyar da ke da shirin tsallakawa nahiyar ta Turai ba bisa ka’ida ba su bude kunne su ji gargadin, domin kuwa gwamnatinsa baza ta goyi bayan duk wani yunkurin karya doka ba.

Haka zalika Muhammadu Buhari ya sha alwashin dawo da ‘yan Najeriyar da suka makale a Libya a kokarinsu na tsallakawa nahiyar Turai ta tekun Maditerranean.

A nata jawabin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yaba da karsashin matasan na Najeriya inda ta ce kulawa kawai su ke bukata daga gwamnotoci wajen samr musu da abubuwan yi don samun rayuwa mai inganci.

Shugabannin biyu sun kuma tattauna babban zaben Najeriyar mai zuwa na shekarar 2019 inda Merkel ta yi fatan gudanar da sahihi kuma ingantaccen zabe ba tare da magudi ko tauye hakki ba.

Merkel ta yaba da kokarin gwamnati mai ci a yakin da ta ke da ta’addanci tare da fatan dorewar alaka a tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.