Isa ga babban shafi
Najeriya-Amnesty

Amnesty ta bukaci kawo karshen kame ba bisa ka'ida ba a Najeriya

Kungiyar kare Hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta zargi gwamnatin Najeriya da kama mutane ta na tsarewa da kuma batar da su ba tare da kai su gaban shari’a ba.

A cewar Kungiyar ta Amnesty baya ga tarin jama'ar da Najeriyar ke kamewa ba bisa ka'ida ba, akwai kuma tarin mutane da ta batar da su ciki har da mabiya shi'a 600.
A cewar Kungiyar ta Amnesty baya ga tarin jama'ar da Najeriyar ke kamewa ba bisa ka'ida ba, akwai kuma tarin mutane da ta batar da su ciki har da mabiya shi'a 600. Logo AI
Talla

Sanarwar kungiyar ta ce gwamnatin Najeriya na amfani da matakin wajen rufe bakin yan adawa da kuma tilasta tsoro kan fararen hula.

Daraktan kungiyar Osai Ojigho ta bada misali da kama wani dan jarida Abiri Jones da hukumar DSS ta yi, wanda gwamnatin ta ki amincewa har sanda aka kwashe shekaru 2 ana tsare da shi.

Kungiyar ta kuma bukaci gwamnatin Najeriya ta yi bayani kan tarin mutanen da ake zargin cewar ta batar da su, cikin su harda mabiya Shia’a kusan 600.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.