Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Zaben Zimbabwe: Mnangagwa ya nada kwamitin bincike

Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya nada tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu, Kgalema Motlante domin jagorancin kwamitin da zai gudanar da bincike kan tashe-tashen hankulan da aka samu bayan zabe da suka haddasa asarar rayuka.

Shugaban Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa ya lashe zaben kasar na ranar 30 ga watan Yuli
Shugaban Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa ya lashe zaben kasar na ranar 30 ga watan Yuli REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Kwamitin mai wakilai 7 zai duba rawar da sojoji suka taka ta hanyar bude wuta kan fararen hula wanda ya kaiga kashe mutane 6.

Sauran ‘yan kwamitin sun hada tsohon Sakatare Janar na kungiyar kasashe renon Ingila, wato Commonwealth, Emeka Anyaoku da wani lauya dan Birtaniya Rodney Dixon da tsohon hafsan sojin Tanzania Davis Mwamunyange da wasu malaman jami’oin Zimbabwe biyu da lauya guda.

Ana kallon zaben a matsayin wanda zai bude sabon babi a Zimbabwe tare da janyo hankulan masu zuba jari daga kasashen ketare bayan kawar da mulkin Robert Mugabe da ya shafe shekaru 37 akan karaga.

Sai dai zaben ya gamu da cikas saboda harbe-harben sojoji da kuma zarge-zargen tafka magudi

Shugaba Mnangagwa ya ce, kwamitin binciken zai gano wadanda suka aikata laifin da kuma manufarsu ta yin haka.

An bayyana Mnangagwa a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaben na ranar 30 ga watan Yulin da ya gabata, yayin da ya zargi jam’iyyar adawa ta MDC da kitsa tashin hankalin da aka samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.