Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo

Yan takara shida a Congo sun garzaya Kotu

Daukacin yan takarar zaben shugaban kasar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo 6 da hukumar zabe ta haramtawa shiga takarar zaben da za’ayi a watan Disamba sun daukaka kara zuwa kotun koli.

Jean-Pierre Bemba daya daga cikin yan takara da hukumar zaben Congo ta yi watsi da takarar su
Jean-Pierre Bemba daya daga cikin yan takara da hukumar zaben Congo ta yi watsi da takarar su REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Cikin masu kalubalantar hukuncin harda tsohon shugaban yan tawaye Jean Pierre Bemba da tsoffin Firaminista 3 da suka yi aiki a karkahsin shugaba Joseph Kabila, wato Samy Badibanga da Adolphe Muzito da Antoine Gizenga, sai kuma mace guda Marie-Josee Ifoku Mputa.

Ana saran kotun ta saurari karar yan takarar, yayin da hukumar zabe zata wallafa yan takarar da zasu shiga zaben ranar 19 ga watan Satumba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.