Kotu ta gurfanar da mataimakiyar shugaban kotun kolin Kenya
Yan Sanda a Kenya sun sanar da kama mataimakiyar shugaban kotun kolin kasar Philomena Mwilu saboda zargin da ake mata na karbar cin hanci da rashawa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Mai shari’ar na daga cikin alkalan kotun koli 7 da suka soke zaben shugaban kasar zagaye na farko da shugaba Uhuru Kenyatta ya lashe a watan Agustan bara, wanda ya haifar da rikici a kasar.
Darakatan gabatar da kara, Noordin Haji ya ce akwai sheidun dake nuna yadda mai shari’ar ta saba ka’idar aiki domin biyan bukatun kan ta da suka hada da karbar kudade da kyaututtuka da kuma kaucewa biyan haraji.
Kotu ta bada belin ta bayan gurfanar da ita a gaban shari’a akan kudi sule miliyan 5.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu