Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Mnangagwa ya karbi rantsuwar shugabancin Zimbabwe

Yau Lahadi aka rantsar da Emmerson Mnangagwa a matsayin sabon shugaban Zimbabwe bayan lashe zaben shugabancin kasar da ya gudana a watan Yuli, zabe na farko bayan shudewar mulkin shekaru 37 na Robert Mugabe.

Emmerson Mnangagwa, yayin karbar rantsuwar soma shugabancin Zimbabwe a karo na biyu. 26 ga Agusta, 2018.
Emmerson Mnangagwa, yayin karbar rantsuwar soma shugabancin Zimbabwe a karo na biyu. 26 ga Agusta, 2018. REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Bayan karbar rantsuwar kama aiki a filin wasanni da ke birnin Harare, Mnangagwa, ya sha alwashin kare mutunci da hakkokin ‘yan Zimbabwe, inda ya ce gwamnatin za ta mayar da hankali sosai wajen dai-daita tattalin arzikin kasar da ya dade da durkushewa.

Mnangagwa ya kuma yi alkwarin kadamar da bincike kan rikicin siyasar kasar da ya biyo bayan zanga-zangar 'yan adawa da suka ki amincewa da sakamakon zaben shugabancin kasar, bayan kammala shi.

A jiya Asabar ne dai, yayin mayar da martani kan hukuncin kotun kolin Zimbabwe da ta tabbatar da nasarar Mnangagwa, Jargoran ‘yan adawa Nelson Chamisa ya sha alwashin cigaba da kalubalantar sakamakon zaben, tare da kuma jagorantar jerin zanga-zangar lumana a kasar.

Tsohon shugaban Zimbabwe Robert Mugabe bai samu halartar bikin rantsar da Mnangagwa ba, sai dai 'yarsa  Bonu ta wakilci tsohon shugaban, wadda a baya ta bayyana Mnangagwa a matsayin maci amana, bayan kawar da mulkin mahaifinta.

Idan za'a iya tunawa dai Shugaba Mnangagwa wanda ya tsayawa jam'iyyar ZANU-PF mai mullki takara, ya lashe kashi 50.8 na kuri'un da aka kada a zaben da ya gudana a ranar 30 ga watan Yuli, yayinda jagoran 'yan adawa Nelson Chamisa ya samu kashi 44.3 na kuri'un.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.