Isa ga babban shafi

Jami'an lafiya a Congo sun soma gwajin sabon maganin Ebola

Jami’an lafiya a Jamhuriyar Congo sun sanar da soma gwajin amfani da wasu sabbin magunguna da domin kawo karshen cutar Ebola da ta sake bulla a kasar karo na 10.

Wasu jami'an lafiya da ke lura da masu fama da cutar Ebola a Jamhuriyar Congo.
Wasu jami'an lafiya da ke lura da masu fama da cutar Ebola a Jamhuriyar Congo. Florence Morice / RFI
Talla

Matakin da jami’an suka bayyana a yau Asabar ya zo ne a dai dai lokacin da wata kididdiga da suka fitar ta nuna cewa, yawan wadanda suka hallaka sakamakon kamuwa da cutar ta Ebola ya kai mutane 67.

Sai dai ministan lafiyar Jamhuriyar Congo Ilunga Kalenga ya ce zuwa yanzu sun yi nasarar ganin warkewar akalla mutane 11 daga cikin wadanda suka kamu da cutar a baya bayan, sakamakon jarraba wasu magunguna.

A farkon watan Agustan da muke ciki cutar Ebola ta sake bulla a Jamhuriyar Congo a arewacin lardin Kivu mai fama da hare-haren mayakan kungiyoyin ‘yan tawaye daban-daban, lamarin da ya takaita ayyukan jami’an lafiya da na agaji, wadanda wasunsu yanzu haka ke hannun mayakan suna garkuwa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.