Kamaru
'Yan adawa sun gaza tsayar da dan takara daya a Kamaru
Watanni biyu kafin zaben shugabancin kasar Kamaru, ga alamu abu ne mai wuya a cimma jituwa tsakanin ‘yan adawa domin tsayawar da mutum daya da zai wakilce domin fafatwa da shugaba Paul Biya a wannan zabe da za a yi ranar 7 ga watan oktoba mai zuwa.
Wallafawa ranar:
Talla
Paul Biya mai shekaru 85 a duniya, ya share tsawon shekaru 35 yana mulkin kasar ta Kamaru, yana shirin karawa ne da wasu ‘yan takara 7 daga jam’iyyun adawa, wadanda suka gana sau da dama a tsakaninsu domin fitar fitar da mutum daya da zai wakilce su amma ba su cimma matsaya ba a kai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu