Isa ga babban shafi
Najeriya

HRW ta ce ana muzgunawa 'yan jarida a Najeriya

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta zargin hukumomin tsaron Najeriya da tursasawa ‘yan jarida a kasar, inda kungiyar ke cewa matakan da hukumomin tsaron ke dauka sun haddasa tsoro ga ma’aikatan yada labarai.

Jami'an hukumar tsaro na (DSS), Nigeria.
Jami'an hukumar tsaro na (DSS), Nigeria. guardian.ng
Talla

Misis Anietie Ewang daya daga cikin manyan jami’ai a Kungiyar, ta ce kama dan jarida tare da jefa shi a gidan yari, ba abin da zai haifar face komabaya ta fannin bai wa jama’a damar sanin abin da ke faruwa.

Human Rights Watch ta ce yanzu haka akwai wani dan jarida mai suna Jones Abiri da ke aiki da Jaridar Weekly Source Newspaper, wanda hukumar DSS ta cafke shekaru biyu ba tare da an yi masa shari’a bisa zargin cewa yana da alaka da ‘yan bindiga na yankin Niger Delta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.