Magoya bayan Cisse sun yi zanga-zanga a Bamako
Daruruwan magoya bayan dan takarar ‘yan adawa a zaben shugabancin Mali, Souma’ila Cisse, sun gudanar da zanga-zanga jiya Asabar a babban birnin kasar Bamako, domin nuna rashin amincewa da sakamakon da ya baiwa shugaba mai ci Ibrahim Boubacar Keita nasara da gagarumin rinjaye.
Wallafawa ranar:
Magoya bayan na Cisse sun gudanar da zanga-zangar ce cikin sa idon ‘yan sandan kwantar da tarzoma, wadanda suka kasance cikin shirin ko ta kwana.
Tuni dai Cisse ya shigar da kara kotun kolin kasar domin kalubalantar zaben da ya ce an tafka magudi a cikinsa.
Sai dai tawagar da ta sa ido kan zaben na Mali daga kungiyar tarayyar turai da wasu takwarorinta na ciki da wajen kasar, sun ce duk da an fuskanci tangarda a wasu wuraren yayin gudanar da zaben, babu wata shaida da ke nuna an tafka magudin da ‘yan adawa ke zargi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu