Isa ga babban shafi
Sudan

Yara 22 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Sudan

A Sudan, yara 22 ne suka rasa rayukansu a daidai lokacin da suke kokarin tsallaka kogi na Nil a kan hanyar su ta zuwa makaranta.

Wani kwale-kwale dauke da jama'a a Ubangui
Wani kwale-kwale dauke da jama'a a Ubangui ISSOUF SANOGO/AFP
Talla

Mutanen sun hadu da ajalinsu ne lokacin da suke kokarin tsallaka kogi na Nil ta hanyar amfani da kwale-kwale domin zuwa makaranta.

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, kuma mai magana da yawun rundunar 'yan sanda ya sheidawa Kamfanin Afp cewa, wata mata ta rasu a dai-dai lokacin da kwale-kwale ya jirkice.

Tuni dai aka tabbatar da mutuwar yara 22 yan makaranta ana ci gaba da neman gawarwakin wadanan dalibai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.