Isa ga babban shafi
Kamaru

An samu ci gaba a yaki da Boko Haram a Kamaru

Kungiyar Internationnal Crisis Group a Kamaru ta bayyana cewa an samu ci gaba a yakin da hukumomin kasar ke yi da yan kungiyar Boko Haram.

Tambari na kungiyar Internationnal Crisis Group
Tambari na kungiyar Internationnal Crisis Group International Cancer Genome Consortium
Talla

Kungiyar Internationnal Crisis Group a wannan sabon rahoto da ta fitar ta bayyana irin ci gaba da aka samu tareda bukatar Gwamnatin kasar Kamaru ta bulo da wani tsari da zai taimaka domin samarwa tsofin yan kungiyar Boko Haram ayukan yi.

Kungiyar Internationnal Crisis Group dake mayar da hankali zuwa batuntuwan da jibanci rikice-rikice ta fitar da wasu sabin alkaluma dake nuna irin ci gaba da aka samu a yakin da Kamaru ke yi da yan kungiyar Boko Haram.

A yau talata kungiyar ta hakikanta cewa an samu gaggarumin ci gaba duk da cewa mayakan kungiyar ta Boko Haram na ci gaba da yi barrazana, tsawon Shekaru biyu an samu mutuwar mutane da dama, kama daga farraren hula, sojoji.

Kungiyar ta bukaci hukumomin Kamaru na ganin sun zare dantse domin tabbatar da cikkaken tsaro a yankunan arewacin kasar.

An samu ragowa hare-haren yan kungiyar Boko Haram a dan tsakanin nan ,a cewar kungiyar akwai rahotanni dake tabbatar da cewa yan kasar Kamaru da dama ne suka shiga kungiyar ta Boko Haram daga shekaru na 2012 zuwa 2016.

A karshe kungiyar ta bukaci gwamnatin Kamaru da ta bulo da wani shiri da zai taimakawa tsofin mayakan Boko Haram da suka mika kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.