Mali
Guterres ya bukaci 'yan takarar zaben Mali su kai zuciya nesa
Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Turai sun bukaci taka tsan tsan a Mali, bayan da dan takaran zaben shugaban kasa daga bangaren yan adawa, Soumaila Cisse ya ce ba zai amince da sakamakon zaben kasar ba.
Wallafawa ranar:
Talla
Sakatare Janar Antonio Guterres ya bukaci bangarorin biyu da su kwantar da hankalin har zuwa lokacin da za’a bada kammalallen sakamakon zaben, yayin da kungiyar kasashen Turai ta bukaci bangarorin da su kaucewa bayyana sakamakon na kashin kan su.
Tuni Cisse ya bukaci magoya bayan sa da su kwatowa kan su yanci kan sakamakon zaben.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu