Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Yakubu Datti kan zargin yada kalaman batancin da gwamnatin Plateau ke yi kan kafafen Rediyo masu zaman kansu

Wallafawa ranar:

Gwamnatin Jihar Plateau da ke Najeriya ta yi zargin cewar yanzu haka wasu kafofin rediyo masu zaman kan su da ke aiki a Jihar na yada kalamun batancin da ke iya haifar da tashin hankali.Gwamnati ta bayyana haka ne bayan gabatar da korofi kan hukumar sadarwa ta kasa, NBC, inda ta bukaci tayi amfani da karfin doka wajen hukunta wadannan tashoshi. Bayan gabatar da korafin, mun tattauna da kwamishinan yada labaran Jihar, Yakubu Datti, inda muka tambaye shi ko me yayi zafi haka?

Jihar ta Plateau wadda ba ta jima da farfadowa daga rikicin baya-bayan nan da ya hallaka tarin jama'a ba, gwamnati na ganin kalaman na iya haifar da tashe-tashen hankula.
Jihar ta Plateau wadda ba ta jima da farfadowa daga rikicin baya-bayan nan da ya hallaka tarin jama'a ba, gwamnati na ganin kalaman na iya haifar da tashe-tashen hankula. AFP
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.