Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo-Ebola

Mutane 4 sun kara mutuwa sakamakon Ebola a Jamhuriyar Congo

Hukumomin Lafiya a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo sun sanar da cewar an sake samun Karin mutane 4 da suka rasa rayukan su sakamakon kamuwa da cutar Ebola, makonni biyu bayan an sanar da magance cutar da ta hallaka mutane 33.

Yau Laraba ake saran hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya za ta fara aikin bayar da rigakafin Ebola a kasar ta Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo.
Yau Laraba ake saran hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya za ta fara aikin bayar da rigakafin Ebola a kasar ta Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo. AFP Photo/Junior D. Kannah
Talla

Sanarwar ma’aikatar lafiyar ta ce mutanen 4 sun mutu ne a Beni da ke Arewacin Kivu, abinda ya kawo adadin wadanda suka mutu yanzu zuwa 7.

Alkaluman da hukumomi suka bayar sun nuna cewar, mutane 43 ne ake zargin sun kamu da cutar, yayinda aka tabbatar da 16 daga ciki, sai kuma 27 wadanda har yanzu ake da shakku kan su.

Yau Laraba ake saran hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya za ta fara aikin bayar da rigakafin cutar a yankin da aka samu barkewarta a kasar ta Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.