Isa ga babban shafi
Ghana

Hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF ta dakatar da alkalan wasa 7 yan Ghana daga aiki

Hukumar shirya wasannin kwallon kafar nahiyar Afrika CAF dake da ofishinta a birnin Cairon kasar Masar, ta bayyana dakatar da wasu alkalai 7 da wani mai horarwa guda dan kasar Ghana daga ci gaba da gudanar da ayukansu, sakamakon bankado cewa suna da hannu a wata badakalar cin hancin da kafofin yada labarai suka yi ta ya madidi da ita

alamar hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF
alamar hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF RFI Kiswahili
Talla

A ranar 5 ga wannan wata na ogusta ne, alkalan sashen ladabtarwa na hukumar ta CAF suka gudanar da wani taro, inda suka nazarta zargin da kafofin yada labarai suka   wadannan jami’ai na CAF.

A cikin wani kundi da ya fallasa badakalar, da ake kira  "Number 12", wani dan jarida mai bincike na kasar Ghna Anas Aremeyaw Anas, ya kafa tarko ga alkalan wasa da dama na kasar Ghana,  da ma wasu na nahiyar, ta hanyar yi masu tayin basu cin hanci

Yanzu haka dai, jam’ian hukumar yan kasar Ghana 8 ne aka dakatar daga  alkalanci d na tsawon shekaru 10 da suka hada da David Laryea, mataimakin alkalin wasa, da aka haramtawa aikin har iya rayuwarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.