Isa ga babban shafi

Tashin hankali ya barke a gabashin Habasha

Tashin hankalin da ya barke a lardin Somali da ke gabashin kasar Habasha a jiya Asabar, sakamakon girke dakarun sojin kasar a babban birnin yankin, yana ci gaba da bazuwa zuwa wasu sassansa, inda ake fasa shaguna da sace kayayyaki.

Wasu dakarun sojin Habasha da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Somalia.
Wasu dakarun sojin Habasha da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Somalia. REUTERS/Shabelle Media
Talla

Tun a daren ranar Juma’ar da ta gabata ne sojin Habasha suka kutsa kai cikin babban birnin lardin na Somali, jijiga, wanda ake kyautata zaton ana nufin kama manyan jami’an gwamnatin lardin ne, ko da yake har yanzu ma’aikatar tsaron Habasha ba ta ce komai ba dangane da dalilin girke dakarun nata.

Lardin na Somali ya shafe akalla shekaru 30 yana fama da rikici, inda sojin Habasha ke yakar kungiyar ‘yan tawayen Ogaden (ONLF) da aka kafa a shekarar 1984, da ke neman ballewar yankin na Somali daga kasar.

A shekarar 2017 da ta gabata, tashin hankali yayi kamari a yankin na Somali da ke makwabtaka da yankin Oromiya, wanda zuwa yanzu, yayi sanadin raba dubban fararen hula da muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.