Isa ga babban shafi

Zimbabwe: 'Yan adawa 24 sun gurfana a gaban kotu

Yau Asabar wasu magoya bayan jam’iyyar adawa ta MDC a Zimbabwe suka gurfana a gaban kotu, bisa zarginsu da haddasa kazamin rikicin da ya biyo bayan zaben shugabancin kasar.

Wasu daga cikin 'yan adawa da jami'an tsaro suka kama a hedikwatar jam'iyyar adawa ta MDC a birnin Harare. 4 ga watan Agsuta, 2018.
Wasu daga cikin 'yan adawa da jami'an tsaro suka kama a hedikwatar jam'iyyar adawa ta MDC a birnin Harare. 4 ga watan Agsuta, 2018. REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Gurfanar mutanen 24 da jami’an tsaron Zimbabwe suka kame a hedikwatar babbar jam’iyyar adawar ta MDC, ya zo ne kwana guda bayan da hukumar zaben kasar ta bayyana shugaba mai ci Emmerson Mnangagwa a matsayin wanda ya lashe zaben.

Sai dai, dan takarar, yan adawa na MDC, wato Chamisa ya yi watsi da sakamakon zaben, tare da ikirarin an tafka magudi a cikinsa.

Akalla mutane 6 ne suka rasa rayukansu yayin rikicin da ya tashi, bayan kammala kada kuri’a, a lokacin da jami’an sojin Zimbabwe suka bude wuta kan dandanzon ‘yan adawar da ke zanga-zanga.

A halin yanzu shugaba Mnangagwa, wanda ya zargi ‘yan adawa da haddasa tashin hankalin, ya bada umarnin kafa wani kwamiti mai zaman kansa, domin gudanar da bincike kan zargin da kungiyoyin fararen hula ke wa sojin kasar na yin amfani da karfi fiye da kima kan ‘yan adawa, lamarin da ya kai ga hasarar rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.