Isa ga babban shafi

Magoya bayan Katumbi sun sha alwashin maida gwaninsu gida

Magoya bayan, jagoran ‘yan adawa a Jamhuriyar congo, Moise Katumbi, sun sha alwashin babu abinda zai hana gwaninsu komawa gida domin taka takara a zaben shugabancin kasar da zai gudana a karshen wannan shekara.

Jagoran 'yan adawa a Jamhuriyar Congo Moise Katumbi.
Jagoran 'yan adawa a Jamhuriyar Congo Moise Katumbi. Yasuyoshi CHIBA / AFP
Talla

Alwashin ‘yan adawar ya zo ne bayan da a jiya Juma’a gwamnatin jamhuriyar Congon ta haramtawa Katumbi shiga kasar.

Jami’an tsaron kasar sun ce an dauki matakin kan jagoran ‘yan adawar ne saboda zarginsa da yunkurin cin amanar kasa ta fuskar tsaro.

Yayin da suke jaddada kudurinsu a yau Asabar, dubban magoya bayan Katumbi, sun ce za su iske shi a garin Kasumbalesa a Zambia, wanda ke kan iyakar kasar da jamhuriyar Congo su maida shi gida, kana kuma su mika takardar takararsa kafin wa’adin karshe na ranar Laraba mai zuwa.

Tun a watan Mayu na shekarar 2016, Katumbi ya yi gudun hijira zuwa kasar Belgium, sakamakon sabanin da suka samu da shugaba Joseph Kabila, wanda a yanzu ya shafe shekaru 17 yana mulkin Jamhuriyar Congo.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.