Isa ga babban shafi
Mali

Za a karawa tsakanin IBK da Cisse a zagaye na biyu a Mali

Hukumar Zabe a kasar Mali tace za’a gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu ranar 12 ga wannan watan tsakanin shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita da babban dan adawa, Soumaila Cisse.

Ibrahim Boubacar Keïta zai karawa da Soumaïla Cissé a zaben ranar 12 ga watan agusta 2018
Ibrahim Boubacar Keïta zai karawa da Soumaïla Cissé a zaben ranar 12 ga watan agusta 2018 STR, ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Ministan kula da yankunan kasar, Mohammed Ag Erlafk ya shaidawa al’ummar kasar cewar, sakamakon zaben da akayi zagayen farko ya nuna cewar, shugaba Ibrahim Boubacar Keita ya samu kusan kashi 42 na kuri’un da aka kada, yayin da Cisse ya samu kusan kashi 18.

Sakamakon ya nuna cewar, dan kasuwa Aliou Diallo ya samu kusan kashi 8 na kuri’un da aka kada, yayin da tsohon ministan sufuri, Cheikh Modibo Diarra ya samu kashi sama da 7 da rabi.

Yan takara 24 suka fafata a zaben, yayin da masu kada kuri’u sama da kashi 43 suka shiga zaben a tashoshi 23,000.

Rahotanni sun ce zaben bai gudana a mazabu 700 saboda matsalolin tsaro, duk da dakarun Majalisar Dinkin Duniya 15,000 da dakarun Faransa 4,500 da kuma sojojin rundunar G5 Sahel dake aiki a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.