An hana Moise Katumbi komawa gida Congo
Mahukunta a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo sun hana wa daya daga cikin masu adawa da shugaban kasar wato Moise Katumbi tsallaka iyakar kasar domin komawa gida.
Wallafawa ranar:
Katumbi, wanda ya share tsawon kwanaki a Afrika ta Kudu, da farko ya nemi a ba shi izinin komawa kasar ta hanyar amfani da jirgin sama mallakinsa amma aka hana shi, daga nan ne kuma ya yi yunkurin tsallaka iyaka ta kasa domin isa a birnin Lubumbashi amma aka kange shi.
Katumbi mai shekaru 53 a duniya, yana fatan komawa gida domin tsayawa takarar neman shugabancin kasar a zabe mai zuwa, to sai dai kafin nan mahukunta sun yi barazanar cafke shi matukar ya sanya kafa a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu